Buhari ya bayar da umurnin gina gidaje 10,000 a jihar Borno

Buhari ya bayar da umurnin gina gidaje 10,000 a jihar Borno

- Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki kwakwarar mataki don rage radadin wahalar da mutanen da ke sansanin 'yan gudun hijira suke ciki a Borno

- Shugaban kasar a ranar Juma'a 10 ga watan Janairu, ya bayar da umurnin gina gidaje 10,000 a jihar Borno

- Baya ga haka, Gwamna Babagana Umaru Zulum ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijirar inda ya taimaka wurin raba musu bargo da sauran kayan sanyi da zai taimaka musu a wannan yanayin na hunturu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da kwangilar gina gidaje 10,000 a jihar Borno a cikin yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na farfado da jihar bayan barnar da ta'addancin Boko Haram ya yi.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a 10 ga watan Janairu a shafinsa na Twitter.

Shugaban kasar ya yi wannan umurnin ne bayan Zulum ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu inda ya kwana a can yana taimakawa wurin rabon kayan tallafi ga kimanin iyalai 1675.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

Gwamnan ya kuma yi rabon barguna da daduma ga 'yan yi wa kasa hidima a jihar don taimaka musu magance sanyi a wannan yanayin na hunturu.

Ya kuma tabbatarwa 'yan gudun hijirar cewa yana nan kan bakansa na kokarin ganin an mayar da su garuruwansu idan an gama gine-gine.

Kazalika, Zulum ya yi wa 'yan gudun hijiran alkawarin cewa gwamnatin tarayya na iya kokarin ta don ganin ta kawoi karshen ta'addanci a jihar da sauran sassan kasar.

Gwamnan jihar na Borno ya kuma yabawa rundunar sojojin Najeriya kan matakin da ta dauka na gudanar da bincike kan zargin karbar kudade a hannun matafiya da ake ce sojoji na yi.

Legit.ng ta gano cewa Zulum ya yi wannan jawabin ne a daren Litinin 6 ga watan Janairu bayan mai kula da fanin yada labarai na soji, Aminu Iliyasu ya fitar da sanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel