'Yan bindiga sun kashe sojan saman Najeriya a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe sojan saman Najeriya a Kaduna

'Yan bindiga sun kai wa wani sojan saman Najeriya (NAF) hari a Unguwan Yako a hanyar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Sojan mai suna Mukhtar Ibrahim ya mutu sakamakon raunin da 'yan bindigan suka masa yayin harin kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Sanarwar da direktan yada labarai na NAF, Commodore Ibikunle Daramola ya fitar a ranar Jumaa ta ce, "Daya daga cikin jami'in mu ya rasu yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin.

"Za a birne marigayin, Mukhtar Ibrahim a yau kamar yadda koyarwar addinin musulunci ta tanada yayin da sauran da suka jikkata kuma suna asibitin NAF a Kaduna suna samun kulawa."

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

Daramola ya ce shugaban sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, a madadin dukkan ofisoshi, sojoji maza da mata da maaikatan NAF suna mika sakon taaziyyarsu ga iyalen jarumin da ya riga mu gidan gaskiya.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun tare matfiya a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri sun yanka mutum uku sun kuma yi awon gaba da wasu fasinjoji bakwai.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis 9 ga watan Janairu kamar yadda wata majiya daga kungiyar direbobi da kuma wasu fasinjoji da suka tsira suka bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel