2023: Matasan Najeriya za mu mika wa mulki - Buhari

2023: Matasan Najeriya za mu mika wa mulki - Buhari

- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ko shugabannin yanzu suna so ko ba su so, dole wata rana matasa za su mika wa mulkin kasar

- Hakan yasa Shugaba Buhari ya bukaci matasan Najeriya su shirya kansu domin akwai nauyi masu yawa na mulki da zai hau kan su

- Shugaban kasar ya ce idan dai ana maganar gina kasa ne babu wanda za a raina gudun mawar da zai iya bayar wa

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 10 ga watan Janairu ya ce matasan Najeriya su kasance cikin shiri domin karbar mulki a kasar nan.

Da ya ke jawabi ga taron shugabanin matasa na jam'iyyar All Progress Congress (APC) daga dukkan sassan kasar da suka kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja, Shugaba Buhari ya ce maganar gaskiya itace dole wata rana matasa za a mika wa mulki.

Shugaban kasar ya ce wannan babban nauyi ne da ya kamata matasan su shirya karba.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

Da ya ke misali da yakin basasan Najeriya da Biafra da ya yi sanadiyar rasa rayuka masu yawa, a cewar shi kimanin miliyan biyu, Buhari ya ce Najeriya ta koyi darasin ta inda ya ce kowa na da amfani wurin gina kasa.

Ya ce: "Babu shakka, wata ranar dole ku ne za ku karbi ragamar mulki a kasar nan saboda haka ya kamata ku kasance cikin shiri na daukan wannan babban nauyin.

"Ya kamata ku shirya karbar mulki. Wasu kungiyoyi za su bijiro da batun kabila da addini amma ya kamata ku kasance masu hangen nesa."

Idan ba a manta ba, Legit.ng ta kawo muku rahoto inda Pastor Tunde Bakare ya ce ya kamata Shugaba Buhari ya zabi wanda zai gaje shi saboda ya cigaba da ayyukan alheri da ya fara.

Amma, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen yada labarai, Femi Adesina ta ce Buhari ba zai zabi wanda zai maye gurbinsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel