Gwamna Mohammed ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi 2, ya bada dalili

Gwamna Mohammed ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi 2, ya bada dalili

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, ya amince da dakatar da kwamitin rikon kwarya na kananan hukumomin Ningi da Darazo na jihar.

An zargi Nura Dan Maishar'a da Gara'u Adamu da amfani da ofisoshinsu ba ta yadda ya dace ba, da kuma taimakawa wajen sare itace a jihar.

A takardar da babban mai bada shawara na musamman a kan yada labarai ga gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ya ce gwamnatin ta gano cewa dukkansu ba su sanya masu ruwa da tsakin kananan hukumonin sauke nauyinsu. Hakan kuwa yayi karantsaye ga wakilci nagari. "An dakatar dasu ne sakamakon halin ko in kula da suka nuna wajen mulkin kananan hukumomin biyu."

Takardar ta cigaba da bayyana cewa, shugaban karamar hukumar Darazo an dakatar dashi ne saboda rashin zuwa ofis, wanda hakan yayi karantsaye ga rantsuwar da yayi na habaka karamar hukumar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun hallaka sojoji 4 a Kaduna

A bangaren shugaban karamar hukumar Ningi na rikon kwarya, an dakatar dashi ne saboda yadda ake sauke bishiyoyi a karamar hukumar, kuma ya zuba ido ba tare da daukar wani mataki ba. Hakan kuwa yaci karo da rantsuwar da yayi na shawo kan karatowar hamada da zai shawo kanta da sauran matsalolin karamar hukumar.

Takardar tace an dakatar da shugabannin kananan hukumomin ne don bada damar bincike mai kyau. An kuma basu umarnin mika karagar mulkin kananan hukumomin ga mataimakansu tare da duk wata kadarar karamar hukumar dake hannunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel