Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun hallaka sojoji 4 a Kaduna

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun hallaka sojoji 4 a Kaduna

Sojoji hudu ne suka rasa rayukansu bayan da 'yan bindiga masu tarin yawa suka kai musu hari a Unguwan Yako, kusa da Buruku a kan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari. 'Yan bindigar sun bankawa motoci biyu na sojojin wuta a yayin musayar wutar da suka yi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis wajen karfe 3 na yammaci.

Kamar yadda majiyar ta sanar, "Yan bindigar sun fito ne da tarin yawansu kuma sun hari sojojin da aka kawo yankin don tabbatar da tsaro bayan jerin hare-haren da 'yan bindigar ke kaiwa. Sun kashe sojoji hudu kuma sun bankawa motoci biyu na sojojin wuta."

DUBA WANNAN: Kotu ta aike da shugaban NCAC zuwa gidan yari

Majiyar ta kara da cewa, "A yayin da ake ruwan wuta tsakanin sojojin da 'yan bindigar, jirgin sama na yaki ya bayyana inda ya sako bam din da kurmushe 'yan bindigan a take."

Majiyar ta tabbatar da cewa, wata rundunar sojin ta fatattaki 'yan bindigar har zuwa cikin daji.

"Ba ko yaushe suke zama a wajen ba, amma saboda karuwa a hare-haren 'yan bindigar da kuma rashin tsaro da ya addabi yankin, an turo sojojin wajen inda suka gamu da ajalinsu," majiyar ta sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel