Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da harin Plateau

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da harin Plateau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da wani hari da wasu yan bindiga suka kaddamar a karamar hukumar Mangu da ke jihar Plateau.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a Wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cikin jawabin, Garba Shehu ya ce shugaba Buhari na tuntubar Gwamnan jihar, Simon Lalong, sojoji da yan sanda da sauran hukumomin tsaro don bincikar lamarin, sannan kuma ya nemi su kara inganta tsaro don kiyaye sake afkuwarsa a gaba.

Yan bindigan dai sun kashe mutane 12 sannan sun jikkata Wani mutum guda a kauyen Kulben.

Wasu idon shaida sun bayyana cewa yan bindigan sun yi wa kauyen zuwan bazata ne a daren ranar Laraba, inda suka dunga harbi ba kakkautawa.

KU KARANTA KUMA: ASUU ta fadi warwas bayan shugaba Buhari ya tilasta suyi rijista da IPPIS

Hakan ya sa wasu mazauna kauyen tserewa cikin jeji don tsira da ransu.

Rundunar yan sanda ta ce ta tura jami’anta yankin, amma ba a kama kowa kan lamarin ba zuwa yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel