Badakalar $24000: Ba zan taba yin shiru wasu na fadin karairayi a kai na ba – Shehu Sani

Badakalar $24000: Ba zan taba yin shiru wasu na fadin karairayi a kai na ba – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya yi magana a karon farko tun bayan kama shi da hukumar EFCC ta yi a kan zarginsa da damfarar wani hamshakin dan kasuwa a garin Kaduna, Alhaji Sani Dauda ASD Motors $24,000.

Sahara Reporters ta ruwaito Shehu Sani ya musanta zargin ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu bayan kwashe tsawon kwanaki 10 a hannun EFCC, inda yace zargin da ake masa basu da tushe balle makama.

KU KARANTA: Mai dokar barci: An kama masu gadin bututun mai su 20 da laifin satar man fetir

Sani yace ba zai taba yin shiru ba a daidai lokacin da wasu ke yayata karairayi a kansa da nufin bata masa suna domin su halasta kama shi da aka yi. Sanatan yace ya baiwa EFCC duk bayanan da take bukata game da zargin, sa’annan ya kalubalanci EFCC ta tabbatar da zargin idan da gaske take.

“Alhaji Sani Dauda da masu daukan nauyinsa sun gagara gabatar da wata kwakkwarar hujja game da zargin da suke min, an kama ni ne kawai a kan takardar koke mai shafi biyu ba tare da wata hujja ba, an yi amfani da ASD da EFCC ne don shirya labarin damfarar.

“ASD ba shi da ilimin da zai iya gudanar da aikin da aka ba shi. Sun ce na yi damfara, amma kuma sun rufe asusun banki na, suna binciken gidaje na da ofisoshi na, tare da bukatar na bayyana kadarori na, bayan tun a bara na yi hakan bayan na fita daga majalisa.” Inji shi.

Daga karshe, Sanatan ya bayyana cewa bai taba haduwa da Alkalin Alkalan Najeriya ba, balle kuma har ya yi alkawarin nema ma ASD alfarma ta hannunsa.

Da fari dai EFCC ta samu izinin kotu na cigaba da rike Shehu Sani tsawon makonni biyu, sa’annan ta nemi ASD ya bayyana gabanta domin tabbatar da tuhumar da yake yi ma Shehu Sani, amma dai har yanzu EFCC ba bayyana ko ASD ya yi hakan ba ko kuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel