Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

An gurfanar da wani mutum mai matsakaicin shekaru, Boniface Mutuku Munyao a Machakos a kasar Kenya a gaban kotun Majistare da Kangundo a ranar Alhamis 9 ga watan Janairu kan tuhumarsa da laifin zina da karya kafin daga baya ya kashe ta.

Wanda ake tuhumar ya yi zina da karyar ne na karshe a ranar Labara 8 ga watan Janairu kafin daga bisani ya yi amfani da igiya ya sheke karyar har sai da ta mutu. Rahotanni sun bayyana cewa an kama shi ne bayan da makwabta suka sanar da jami'an tsaro cewa suna jin ihun karya da tsakar dare.

An ce makwabtan sun bale kofa sun shiga gidansa bayan wari da ke fitowa daga gidan ya dame su a ranar Alhamis 9 ga watan Janairu. Daya daga cikin makwabtan mutumumin ya shaidawa 'yan sanda cewa:

"Mun tsinci kororon roba da aka yi amfani da su tare da gawar karya a gidansa."

Shugaban 'yan sanda na unguwar da ya goyi bayan labarin da makwabtan suka bayar ya ce:

"An gano shi yana lalata da karya bayan wasu makwabta sun lura cewa wari yana fitowa daga tsohon gidan da kakansa ta bar masa.

"Shi da kansa, ya amsa cewa ya yi lalata da karyar na kwanaki kafin daga bisani ya sheke ta ta mutu. An gano kororon roba da aka yi amfani da su masu yawa a wurin.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

"Wannan abin kunya ne kuma da Ubangiji bai amince da shi ba saboda haka ba za mu lamunci irin wannan ba. Wadanda ke ikirarin mutumin na da tabin hankali su fada mana dalilin da yasa ya yi amfani da kororon roba yayin saduwa da karyar"

Wani basarake da ya yi tsokaci kan lamarin ya ce yana tsamanin mutumin ya sha miyagun kwayoyi ne yayin da ya ke aikata wannan abin kyama da muni.

Sai dai da aka gurfanar da shi a kotu ya musanta zargin da ake masa kuma an bayar da belinsa kan Ksh100. Za a cigaba da sauraron shari'ar a ranar 22 ga watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel