Kotu ta aike da shugaban NCAC zuwa gidan yari

Kotu ta aike da shugaban NCAC zuwa gidan yari

Babban kotun tarayya da ke Maitama a Abuja, a ranar Alhamis ta daure shugban Cibiyar Al'addu na kasa, Olusegun Runsewe kan laifin rashin mutunta umurnin kotu.

Mai shari'a Jude Okeke, yayin yanke hukuncin ya bawa Sufeta Janar na 'yan sanda umurnin ya kamo shi ya mika shi gidan gyaran hali da ke Kuje a Abuja kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Alkalin ya bayar da umurnin a cigaba da ajiye a gidan gyaran halin har zuwa lokacin da "ya canja halinsa na rashin mutunta umurnin kotu".

An bayar da umurnin saka Runsewa a gidan yari ne a ranar Alhamis bayan ya ki biyaya ga umurnin kotu da ta bayar a ranar 15 ga watan Disamban 2017.

Umurnin ya danganci karar da wani kamfani mai suna Ummakalif Ltd ya shigar ne na rufe Arts and Crafts Village da ke Abuja.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

Mai shigar da karar ya yi ikirarin cewa rufe wurin ya saba wa yarjejeniyar da su kayi da ta bashi daman gyara wani bangare na cibiyar.

Ya shigar da karar ne a ranar 21 ga Yunin 2019 inda ya nemi a garkame Runsewe a gidan yari saboda saba wa umurnin da kotu ta bayar a ranar 15 ga watan Disamban 2017 na hana dukkan bangarorin daukan wani sabon mataki.

A cewar mai shigar da karar, umurnin na nufin kada a dauki matakin rufe cibiyar.

Mai shari'a Okeke yayin amincewa da bukatar da mai shigar da karar ya nema na garkame Runsewe a gidan yari ya ce hakan zai zama darasi ga sauran mutane masu kin biyaya ga umurnin kotu.

Mai shari'a Umar Salisu wanda ya yanke hukunci kan karar kafin a daukaka kara a Maris din 2018 ya nuna bacin ransa ga NCAC saboda rufe cibiyar duk da cewa kotu ta umurci kada a aikata hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel