Nafi son Kare na fiye da kowanne mutum a duniyar nan - Toke Mokinwa
- Toke Mokinwa ba bakuwa bace a shafukan sada zumuntar zamani
- Sananniyar ta bayyana cewa tafi son dan kuikuyonta a kan mutane, lamarin da ya kawo mata caccaka
- Wani ya shawarce ta da cewa, duk biyayyar dan kuikuyo ba zai taba maye mata gurbin jama'a ba
Toke Mokinwa ba bakuwa bace a kafafen sada zumuntar zamani.
Toke ta jawo cece-kuce ne a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita saboda ra'ayinta da ta bayyana a kan mazan da ke cin amanar matansu.
Kamar yadda Toke ta bayyana a wallafarta, tace tafi son karenta a kan mutane. "Nafi son dan kuikuyona fiye da yadda nake son mutane."
Wannan abin da ta wallafa ya jawo mata maganganu daban-daban daga jama'a.
KU KARANTA: Tashin hankali: Mata tayi yunkurin sayarwa da matsafa dan kamfen karuwar da mijinta ya kawo gidansu
"Yanmata ki dawo cikin hankalinki. Ba dole dan Adam yayi miki biyayya dari bisa dari ba. Amma dan kuikuyo zai iya miki kuma ba zai taba maye miki gurbin mutane a rayuwarki ba." Cewar wani.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng