PDP ce babbar cikas a mulkinmu – Fadar shugaban kasa

PDP ce babbar cikas a mulkinmu – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta nuna fushinta kan ayyukan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), cewa jam’iyyar ce babbar matsala guda ga shugabanci nagari da chanji a kasar.

Malam Garba Shehu, babban mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai, a Wani jawabi a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Janairu, ya ce babbar jam’iyyar adawar kasar bata da hurumi a harkokin jam’iyya mai mulki wato All Progressives Congress (APC).

Ya ce abun mamaki ne yadda jam’iyyar adawar ke fitar da jawabai tamkar ita ce mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Wani hurumi suke dashi wajen magana game da batan soyayya tsakanin shugaba Buhari da APC? Me suka sani? Wa ya aike su?"

Ya ce ya kamata jam’iyyar ta mayar da hankali kan abunda ya dace idan har tana son a sake daukarta a matsayin babbar jam’iyyar adawa.

KU KARANTA KUMA: APC ba zata shiga zaben mayen gurbi ba a jihar Neja - INEC

A cewarsa babban aiki na gaban duk wanda ke jagorantar jam’iyyar da bata da abun ba yan Najeriya sai rashawa, rashin shugabanci nagari da kuma rabuwar kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel