EFCC ta gaggauta sakin Shehu Sani - SERAP

EFCC ta gaggauta sakin Shehu Sani - SERAP

Kungiyar kula da tattalin arziki ta SERAP a ranar Alhamis tayi kira ga hukumar yaki da rashawa ta EFCC a kan ta hanzarta sakin Shehu Sani, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan zamu tuna, Sani, wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai karo na takwas,, ya shiga hannun hukumar ne a ranar 31 ga watan Disamba 2019 a kan zarginsa da ake da damfarar mamallakin ASD Motors, Sani Dauda, har naira miliyan 7.2.

Amma kuma, SERAP ta zargi EFCC din da yin karantsaye ga dokar Najeriya har da ta kasashen ketare wajen kamawa da killace Sanatan.

Takardar da ta fito daga hannun SERAP din ta ce: "Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gaggauta sakin mai rajin kare hakkin dan Adam din, Sanata Shehu Sani, wanda ta adana sakamakon zarginsa da take da damfara.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda fasto ke amfani da kwallon kafa don cire aljannu

"Cigaban tsare Sani ba tare da an gurfanar dashi ba na nufin an yanke mishi hukuncin abinda ake zarginsa da shi, wanda hakan yayi karantsaye ga dokokin kasar nan da wasu kasashen." in ji ta.

"Cigaba da tsare Sani ya take wannan dokar dake bayyana cewa yana da gaskiya har sai an tabbatar da laifinsa," a cewarta.

"Wannan dokar kuwa na nan a kundin tsarin mulki na 1999. Don haka dole ne EFCC ta binciki Sani a kan zargin da ake masa kuma ta sakesa bayan an kammala binciken tare da biyan kudin beli." ta kara da cewa.

Dokar 'yanci ta bayyana cewa tsare mutum ko kama shi dole ne a bi tsarin doka. Wannan hakkin kuwa shi ke ba mutane kariya daga gwamnati ko kuma cibiyoyinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel