Yadda DSS suka tsareni na tsawon makonni 10 saboda Hanan Buhari bata amsa wayarsu ba lokacin tana Ingila - Matashi

Yadda DSS suka tsareni na tsawon makonni 10 saboda Hanan Buhari bata amsa wayarsu ba lokacin tana Ingila - Matashi

Jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama tare da tsare wani matashi, Anthony Okolie, sakamakon ya sayi wani layin waya na kamfanin sadarwa, MTN, da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi a baya.

Okolie ya sayi layin wayar ne tun a shekarar 2018, shekaru biyu kafin kamun da jami'an tsaro suka yi masa.

An kama shi ne ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, 2019.

Jami'an DSS sun yi awon gaba da Okolie zuwa Abuja kafin daga bisani ya shaki iskar 'yanci a watan Disamba, 2019.

Yayin wata ganawarsa da manema labarai a kan abin da ya faru gare shi, Okolie, ya bayyana cewa an kama shine bayan Hanan Buhari ta yi korafin cewa an yi mata kutse a layin wayarta ta hannu.

"Sun kama ni a garin Asaba, jihar Delta, kafin daga bisani su tafi da ni zuwa ofishinsu na Abuja bayan sun sanar da ni cewa sun kamani ne bisa umarnin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari.

"Bayan sun kaini Abuja, sun sanar da ni cewa sun kamani ne saboda ina amfani da tsohon layin wayar Hanan. Sun yi min tambayoyi a kan yadda na samu layin, na fada musu gaskiya, ba tare da na boye wani abu ba, kuma sun tabbatar da hakan bayan sun karbi bayanaina domin tantance wa," a cewar Okolie.

Yadda DSS suka tsareni na tsawon makonni 10 saboda Hanan Buhari bata amsa wayarsu ba lokacin tana Ingila - Matashi
Okolie
Asali: Facebook

Okolie ya bayyana cewa tabbas ya fahimci cewa wata mace Bahaushiya ta taba amfani da layin saboda ana yawan kiransa a yi masa magana da Hausa ko kuma a aiko masa sakon ko ta kwana (SMS) ko ta dandalin sada zumunta (whatsapp) bisa tunanin cewa Hanan ce. Matashin ya ce bai taba amfani da wani sako ko bayani da ya samu a wayarsa ta hannu ba domin aikata laifi ba, kuma bai san Hanan ba, bai kuma taba ganinta ba har yanzu.

DUBA WANNAN: Radadin canji: Magidanci ya sauya sunan yaronsa daga Buhari zuwa Kwankwaso a Gombe

Da yake amsa tambaya a kan dalili da yasa ba a sake shi ba duk da an tabbatar da bai aikata wani laifi ba, sai ya ce, "sun yi kokarin tuntubar Hanan ta hanyar kiran wayarta, amma sai aka ce tana Ingila tana fama da karatu, a saboda haka bata da lokaci.

"Haka na shafe makonni 10 ina tsare a ofishin DSS dake Abuja saboda ba a samu yin magana da Hanan ba balle a sakeni."

Okolie, dan kasuwa, ya ce daga bisani jami'an DSS sun sake shi bayan ya rattaba hannu a kan wasu takardu, a cikinsu har da wata ta yarjejeniyar cewar ba zai shigar da kara kotu ba a kan abin da ya faru.

Sai dai, ya ce babu abin da zai hana shi garzaya wa kotu domin neman hakkinsa da kuma diyyar asarar da ya tafka a kasuwancinsa yayin da yake tsare a hannun hukumar DSS.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel