APC ba zata shiga zaben mayen gurbi ba a jihar Neja - INEC

APC ba zata shiga zaben mayen gurbi ba a jihar Neja - INEC

Hukumar zabe nai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen jihar Neja ta bayyana cewa jam'iyyar APC ba zata shiga zaben mayen gurbi da za a yi ba a mazabar Agwara dake jihar.

INEC ta bayyana cewa jam'iyyu 12 ne zasu fafata a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Janairu amma babu jam'iyyar APC a cikinsu.

Kwamishinan hukumar INEC a jihar Neja, Farfesa Sauel Egwu, shine wanda ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin gana wa da masu ruwa da tsaki a hedikwatar INEC ta jihar Neja dake Minna, babban birnin jiha.

Ya bayyana cewa jam'iyyun da zasu fafata a zaben sun hada da ACD, ADC, AGA, DA, GPN, KP, PPN, PT, SDP, PDP, APGA da ADP tare da bayyana cewa APC ba zata shiga zaben ba saboda ana kalubalantarta a gaban kotu a kan babban zaben da aka gudanar a 2019.

APC ba zata shiga zaben mayen gurbi ba a jihar Neja - INEC
Shugaban jam'iyyar APC; Adams Oshiomhole
Asali: Facebook

"An kalubalanci jam'iyyar APC a gaban kotu a kan sahihancin dan takarar da ta tsayar a zaben da ya gabata, kuma kotu ta bayar da umarnin a sake gudanar da sabon zabe.

DUBA WANNAN: Tsugune bata kare ba: An fara yi wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu sabuwar barazana

"Doka ta tanadi cewa duk jam'iyyar da bata tantance dan takararta da kyau ba kafin mika takardu da fom dinsa ga INEC ba, ba zata sake shiga zaben maye gurbi ba idan kotu ta kwace kujerar daga hannun dan takararta ba," a cewar Farfesa Egwu.

Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewa hukumar INEC ba zata yi amfani da ma'aikatan wucin gadi ba yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel