Barayi sun saci kaya na makudan kudade a shagon jaruma Samira Saje

Barayi sun saci kaya na makudan kudade a shagon jaruma Samira Saje

- Wasu mutane a Kano wadanda ba a san ko su waye bane sun kai farmaki a shagon fitacciyar jaruma Rukayya Sulaiman Saje

- An kwashe wa jarumar kayan shagonta da suka kai na naira miliyan daya da dubu dari shida

- Anyi amfani da makullan shagon ne aka bude kuma har ana rubuta mata ‘I love you Samira’ a kan teburi

Wasu mutane a Kano wadanda ba a san ko su waye ba sun kai farmaki a shagon fitacciyar jaruma Rukayya Sulaiman Saje, inda suka sace kaya na kimanin naira miliyan daya da dubu dari shida.

Wannan abin bakin cikin ya faru ne a daren Lahadi, 28 ga watan Disamba, 2019.

Rukayya, wacce aka fi sani da Samira Saje, ta shaida wa mujallar fim cewar, "A wannan rana da kai na na kulle shagon da misalin karfe 9 na dare, don dama can tunda na bude shagon, ni ke kullewa.

"A lokacin kuwa duk masu aiki na sun tafi hutun Kirsimeti, yayana wanda shine manajan wajen, bashi da lafiya kusan makonni uku yana gida.

"Da safiyar Litinin, 29 ga watan Disamba 2019, na fito da misalin karfe 10 zan bude shago, na ga an rubuta 'I love you Samira' a kan teburin kashiya. Wannan lamarin kuwa ya bani mamaki.

"Ban kalla inda kayan suke ba sai na shiga dakin gyaran gashi. Na ga taga a bude kuma an daura igiya. Na fara salati. Da gudu na fito. Na gano cewa sunyi amfani da wayar janareto na ne a wurin sauke kayan, sun kulla a jikin taga. Kuma dukkan makullai na suna hannuna.”

KU KARANTA: Jerin abubuwa guda 5 na Kannywood da za su dauki hankulan mutane a shekarar 2020

“Wautar da nayi shine ban taba sauya makullan shagon ba tunda na budeshi. Ko kafin in bude wajen an taba sace min N300,000 lokacin muna gyaran wajen. Gashi yanzu kuma an kwashe min kayan N1,600,000.” In ji shi.

Samira ta ce kayan da barayin suka diba sun hada da talabijin, takalma, agoguna masu tsada wadanda farashin su ya kama daga N25,000 zuwa N35,000 ko N45,000 kowanne daya. Akwai huluna masu tsada da kayan mata da suka hada da jakunkuna uku da takalma, ‘yan kunnaye ma ba a barsu ba.

Samira ta kara da cewa mutum na farko da aka kama shine maigadin wurin shagunan don shine abun zargi na farko. A halin yanzu haka, maganar ta na ofishin ‘yan sanda na ‘State CID’, ana bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel