Tashin hankali: Lauya ta fadi ta a daidai lokacin da ta tona asirin makauniyar bogi

Tashin hankali: Lauya ta fadi ta a daidai lokacin da ta tona asirin makauniyar bogi

- Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya reshen jihar Ekiti na makokin mutuwar shugabar kungiyar ta jihar

- Ana zargin wata makauniyar bogi da lauyar ta bankado da lashe mata kurwa

- Amma dan takarar shugabancin kungiyar na kasa ya musanta zargin, don kuwa ya ce tayi shekaru 35 tana fama da ciwon sikila

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Ekiti, ta bada labarin mutuwar shugabar mata ta kungiyar, Oluseyi Ojo. Marigayiyar ta mutu ne bayan ta tona asirin wata mata mai suna Nzube Ekene dake yawon barace-barace tare da nuna ita makauniya ce, bayan kuma ba hakan bane.

Dan takarar kujerar shugabancin kungiyar ta kasa, Barista Dele Adesina ne ya tabbatar da mutuwarta a ranar Alhamis din makon jiya.

Kafin tonuwar asirin Nzube Ekene, tana sanya tabarau ne a fuskarta inda daya daga cikin 'ya'yanta ke mata jagora zuwa hanyar shataletalen babban titin Fajuyi a Ekiti. Waje ne dake dauke da fitillun bada umarni kuma ababen hawa suna wuce. A hakan take amfani da damar wajen rokon kudi daga masu ababen hawan.

Marigayiya Oluseyi Ojo ce ta bankado sirrin wannan mata da 'yan sanda suka hanzarta kama ta. Sun sa mata ankwa tare da iza keyarta zuwa hedkwatarsu dake garin Ekiti domin ci gaba da bincike.

KU KARANTA: Gargadi: Abubuwa 8 da kowa ya kamata ya kiyaye wajen saka a soshiyal midiya

Mutuwar Lauya Oluseyi Ojo ta razana mutane, domin kuwa an zargi makauniyar bogin da lamushe kurwarta.

Sai dai Lauya Dele Adesina yayi watsi da wannan batun domin yace shekaru 35 kenan da Seyi ke fama da cutar sikila.

"Ta barmu a daidai lokacin da muke gudanar da bikin raba kyautuka ga mabukata domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu." In ji Dele.

Bincike ya tabbatar da cewa makauniyar ta bogi da 'yar ta mai mata jagora na hannun 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel