Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Garba Abubakar a matsayin Rajista Janar na hukumar kula da harkokin kamfanoni.

An tattaro cewa kafin nadin nasa, Mista Abubakar ya kasance Daraktan bin dokoki a hukumar.

Nadin nasa na kunshe ne a cikin wata wasika da aka fitar a ranar Talata dauke da sa hannun Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Abba Kyari zuwa ga ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya.

Hakazalika wasikar na dauke da nadin Mista Ademola Razak Seriki a matsayin Shugaban kungiyar da ke jagorantar hukumar.

“Ku sani cewa wa’adin nadin ya kasance daidai da tsarin dokar harkokin kamfanoni da abokan hulda,” in ji wasikar.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC ba ta da wata marabar akida da manufofi da PDP - Adebayo Shittu

Ku tuna cewa Azuka Azinge ce ke jagorantar hukumar a matsayin mukaddashin shugaba tsawon shekaru biyu da suka gabata har sai da kotun kula da da’ar ma’aikata ta akatar da ita, biyo bayan wani lamari da ya shafi kaddamar da kadarori da wasu rashin gaskiya wacce jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng