Gargadi: Abubuwa 8 da kowa ya kamata ya kiyaye wajen saka a soshiyal midiya

Gargadi: Abubuwa 8 da kowa ya kamata ya kiyaye wajen saka a soshiyal midiya

- Akwai wasu al'amura dake jawowa mutum mutane miyagu marasa son ci gaban shi

- Halayyar mutum na iya kawo mishi masifu tare da hatsarurruka da yawa

- Abinda yafi a yanzu, ballantana da tsaro yayi karanci, shine zama mai sirri

Akwai wasu lamurran rayuwa da ya kamata su zama sirri. Babu amfani a watsa su a kafafen sada zumuntar zamani don suna kawo kalubale ga tsaro. Ga takwas daga ciki don a kiyaye.

1. Adireshin gida: Kada a wallafa adireshin gida a kafafen sada zumuntar zamani don kuwa kana bayyana inda za a iya samun ka ne. Akwai 'yan ta'adda masu yawa da baka sani ba.

2. Inda ake a lokacin: Bada bayanin inda kake babban hatsari yake jefa mutum saboda kowa ya san baya gida.

3. Hoton yara ko bidiyo sanye da kayan makaranta: Kada a kuskura a wallafa bidiyo ko hoton yara da kayan makaranta. Ga masu bukatar satar yara, wannan taimako ne babba.

4. Kada a sa hoton yara tare da sunansu: Yin hakan babban hatsari ne da ake tura yara ciki. Yara basu da wayau, duk wanda ya kira sunansu gani suke ya san su da gaske.

KU KARANTA: Najeriya ce kasar da nake matukar son zuwa a rayuwata - Lil Wayne

5. Kada a wallafa rubutu mai sukar wajen aiki: Yin hakan na iya maka sanadin wajen cin abinci. Baka san inda rubutun zai tafi ba.

6. Kada a wallafa bayani kan inda ake tafiya da kuma lokacin tafiya: Wannan ma babban taimako ne ga masu garkuwa da mutane da 'yan fashi.

7. Wallafa hoto tare da sanar da inda ake babban hatsari ne a halin yanzu da garkuwa da mutane tayi yawa.

8. Wallafa hoton a wajen cin abinci ko kuma gida ana cin abinci kasaitacce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel