Sabbin masarautu: Ganduje ya kalubalanci dattijan Kano a gaban kotu, ya ce akwai mutum miliyan 20 a Kano

Sabbin masarautu: Ganduje ya kalubalanci dattijan Kano a gaban kotu, ya ce akwai mutum miliyan 20 a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano wacce ta samu jagorancin Jastis Nuradeen sagir a ranar Laraba, ta dage sauraron shari'ar da dattawan jihar Kano wadanda suka samu jagorancin Bashir Tofa, zuwa ranar 27 ga watan Janairu.

Dattawan jihar Kano din sun maka Gwamna Abdullahi Ganduje gaban kotu ne a kan kalubalantar kirkirar sabbin masarutu hudu a jihar Kano.

A yayin zaman kotun a ranar Laraba, Gwamnatin jihar Kano ta mika sukar sauraron karar a gaban kotun.

Barista Ibrahim Mukhtar ya bayyana cewa, an kirkiri wadannan sabbin masarautun ne saboda bukatar da jama'a suka bayyana. Kuma yace dattijan ashirin ba zasu soke burin mutane har miliyan ashirin dake jihar ba.

Alkalin mai shari'a, Jastis Nuradeen Sagir, ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Janairu na 2020 don cigaba da sauraron shari'a.

DUBA WANNAN: Jami'an EFCC na can gidan Shehu Sani suna binciken kwakwaf

Idan ba mu manta ba, dattijan jihar Kano din karkashin shugabancin Bashir Tofa, sun maka gwamna Abdullahi Umar Ganduje kotu a kan kirkirar sabbin masarautu.

Sun bayyana cewa, kirkirar sabbin masarautun babu abinda zai kawo sai rabuwar kan jihar.

Mutane da yawa sun zargi kirkirar sabbin masarautun da wani yunkuri na Gwamna Ganduje na rage karfin ikon Sarki Muhammadu Sanusi II.

Amma kuma, an ja hankalin gwamnan da cewa zai lalata tarihin ne mai matukar tushe da asali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel