Yanzu-yanzu: Kotu ta sanar da ranar yanke hukunci kan sabbin masarautun Kano

Yanzu-yanzu: Kotu ta sanar da ranar yanke hukunci kan sabbin masarautun Kano

Wata babbar kotun jihar Kano ta sanar da ranar yanke hukuncin kan karar da wasu dattawan Kano suka shigar na bukatar soke dokan kafa sabbin masarautun Kano hudu da majalisar dokokin jihar tayi.

Alhaji Bashir Tofa tare da wasu dattawan Kano 19 suka shigar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kan kafa sabbin masarautu.

Wadanda aka shiga kotu sune: Gwamnan jihar Kano, Kakakin majalisar dokokin jihar, Majalisar dokokin jihar da kanta, babban Lauyan jihar Kano, sarkin Rano, Tafida Abubakar-Ila; sarkin Gaya, Ibrahim Abdulkadir-Gaya; sarkin Karaye, Dakta Ibrahim Abubakar II; da sarkin Bichi, Aminu Ado-Bayero, da masarautar Kano.

Alkali Nura Sagir ya dage karar zuwa ranar 27 ga Junairu, 2019 domin yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel