Murna ta koma ciki: Za mu sake bude binciken tsohon gwamnan jahar Ribas – EFCC

Murna ta koma ciki: Za mu sake bude binciken tsohon gwamnan jahar Ribas – EFCC

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana cewa za ta sake bude binciken da ta dakatar a kan tsohon gwamnan jahar Ribas, Peter Odili, na satar makudan kudaden jahar.

Mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu ne ya bayyana haka yayin ziyarar daya kai garin Fatakwal, inda yace a yanzu haka suna kalubalantar kariyar da Odili ya samu a gaban kotun kolin Najeriya.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Magu ya yi ma barayin dukiyar jama’a sabon albishir a 2020

Jaridar The Nation ta ruwaito Magu yace akwai hukuncin kotun da ta tabbatar da cewa babu wanda ya isa hana EFCC binciken ko wane mutum, don haka hukuncin da kotun ta yanke na hana EFCC binciken Odili bai inganta ba.

Magu ya kara da cewa hukumar EFCC za ta cigaba da gudanar da bincike a kan manyan laifukan satar dukiyar al’umma a kasar nan, a cewarsa jahar Ribas ce ta biyu cikin jahohin da aka fi tafka laifukan satar duikiyar gwamnati, bayan Legas.

A wani labarin kuma, Malam Ibrahim Magu ya bayyana cewa zasu dauki sabin tsauraran matakai a kan barayin dukiyar jama’a, musamman barayin mai a yankin Neja Delta, inda yace idan suka kammala dabbaka sabbin tsauraran matakan nasu, barayin ba zasu sake samun wani katabus na yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa ba, musamman a cikin sabuwar shekarar 2020.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya fitar, Magu yace: “Bari na yi amfani da wannan daman a gargadi barayin mai masu fasa bututun mai da su daina wannan mugun aiki, a shirye mu ke mu yakesu domin kawo karshen yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa.

“Yankin Neja Delta na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa, don haka hukumar EFCC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar an hukunta dukkanin masu satar mai tare da fasa bututun mai.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel