Yanzu Yanzu: Zababben Ciyaman ya mutu yan sa’o’i kafin tantance shi
- Allah ya yiwa zababben shugaban kwamitin rikon kwarya a yankin karamar hukumar Ipokia da ke jihar Ogun, Saibu Adeosun Mulero rasuwa
- Ya rasu ne yan sa’o’i kadan kafin majalisar dokokin jihar ta tantance shi
- Ya kasance daya daga cikin zababbun shugabannin kwamitin mika mulki na kananan hukumomi 20 a gwamnan Ogun ya zaba
Rahotanni sun kawo cewa Allah ya yiwa zababben shugaban kwamitin rikon kwarya a yankin karamar hukumar Ipokia da ke jihar Ogun, Saibu Adeosun Mulero rasuwa.
Ya rasu ne yan sa’o’i kadan kafin majalisar dokokin jihar ta tantance shi.
Ya kasance daya daga cikin zababbun shugabannin kwamitin mika mulki na kananan hukumomi 20 a jihar Ogun, wadanda Gwamna Dapo Abiodun ya nada a makon da ya gabata.
KU KARANTA KUMA: Iran ta ce Amurkawa 80 aka kashe a harin makamai masu linzami da ta kai
An tattaro cewa marigayin ya shirya tsaf domin tantancewar da za a yi masa a Abeokuta amma sai ya dan kwanta, baccin da bai tashi ba kenan.
An rahoto cewa marigayin ya mutu ya bar mata daya, Mulikat da kuma yara uku.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng