Iran ta ce Amurkawa 80 aka kashe a harin makamai masu linzami da ta kai

Iran ta ce Amurkawa 80 aka kashe a harin makamai masu linzami da ta kai

Rundunar sojin kasar Iran ta sanar da kai hare-hare da makamai masu linzami a kan sansanonin sojojin Amurka da ke garuruwan Irbil da Anbar na kasar Iraki.

Tashar talabijin din kasar Iran ta ce "An harba makamai masu linzami 15, sannan kuma an kashe Amurkawa 80". Kamfanin dillancin labarai na Fars kuma ya fitar da bidiyon yadda aka kai harin.

Sanarwar da Rundunar Sojin Juyin Juya Hali ta Iran ta fitar ta bayyana cewar an kai harin ne domin yin ramuwar gayya ga kisan gillar da Amurka ta yiwa Janar Kasim Sulaimani a ranar Juma'ar da ya gabata a Bagdad Babban Birnin Iraki.

Sanarwar ta ce sun kai hari ta kasa kan sansanin Ayn Al-Asad na Amurka dake Iraki.

Har ila yau sanarwar ta kuma ce idan Amurka ta kuskura ta mayar da martani ga harin to za ta fuskanci ramuwar gayya mafi muni.

KU KARANTA KUMA: Rana ba ta karya: INEC ta sa lokacin da za ayi zabuka 28

Daga karshe ta kuma gargadi kasashen yankin da Amurka take da sansanoni a cikinsu.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Kasar Iran ta yi barazanar ragargazan Izra'ila da Dubai idan har kasar Amurka ta sake kai mata kara bayan ta mayar da martani da daren jiya inda ta kaiwa Sojin Amurka hari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng