Rana ba ta karya: INEC ta sa lokacin da za ayi zabuka 28

Rana ba ta karya: INEC ta sa lokacin da za ayi zabuka 28

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta c eta shirya tsaf don gudanar da zabuka 28 da suka yi saura a fadin jihohi 11 na tarayya.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana hakan yayinda ya ke jawabi ga manema labarai na fadar Shugaban kasa a ranar Talata, 7 ga watan Janairu a Abuja.

Ya yi magana ne jim kadan bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da manyan jami’an hukumar zaben a fadar Villa.

Har ila yau wadanda suka halarci ganawar sun hada da Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu; Darakta Janar na hukumar tsaro na farin kaya (DSS), da Shugaban ma’aikatan shugaban, Abba Kyari.

Farfesa Yakubu ya sanar da cewa INEC ta shirya ranar 25 ga watan Janairu domin gudanar da aikin, inda ya bayyana cewa zabukan guda 28 na daga cikin guda 30 da kotuna suka soke.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun amshe wani gari a Neja, sun fatattaki mutum 2,500

A nashi bangaren, Shugaban yan sandan Najeriya ya bayyana cewa yan sanda na nan a shirye domin hana satar akwatunan zabe da sauran abubuwan magudin zabe.

Dda farko Shugaban kasa Buhari ya umurci INEC da yan sanda da su yiwa yan Najeriya adalci, cewa ya zama dole hukumar ta tabbatar da buga wasan daidai da tsari, ba tare da tsoro ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel