Bidiyon yadda fasto ke amfani da kwallon kafa don cire aljannu

Bidiyon yadda fasto ke amfani da kwallon kafa don cire aljannu

Wani babban fasto a kasar Kenya mai suna Nganga ya saba bai wa jama’a mamaki mai tarin yawa. Mutane da yawa na ganinsa a matsayin mafi kwarewa a drama a cikin fastocin Afirka. Amma kuma sai wani fasto na kasar Uganda ya nuna masa bai san komai ba.

Samuel Kakande, makwafin Nganga ne don kuwa ya aikata abinda yafi na faston kasar Kenyan tsauri. An ganshi da kwallon kafa a yayin bauta a cikin cocin inda yake cirewa jama’a miyagun aljanu.

Kowanne lokaci da faston ya buga kwallon ga daya daga cikin masu bautar dake da miyagun aljanu, sai mai bautar ya tashi tare da faduwa kasa warwas.

Bayan sun fadin ne suke murkususu tare da fita hayyacinsu sannan sai miyagun aljanun da ake magana su fita daga jikinsu.

DUBA WANNAN: Trump ya yi amai ya lashe kan barazanar kai hari wuraren tarihi a Iran

A bidiyon kuwa an nuna sauran masu bautar suna zaune inda suke kallon yadda rayuwar masu aljanun ke dawowa a hankali. Hakazalika masu bautar na tintsira dariya tare da taimakawa ‘yan uwansu tashi.

Duk da cewa kuwa faston ya daure fuskarsa babu ko alamar dariya, amma yana cigaba da umartar miyagun aljanun fita daga jikin mabiyansa.

Kowa ya san faston, matukar ya yi dariya koda kadan ce, toh tabbas a shirya kwasar nishadin da zai iya sa hakarkarin mutum ciwo. A nan Samuel ya cigaba da kallon yadda matukar karfin ikonsa ke fitar da miyagun aljanu daga jikin jama’a.

Babban faston ya yadda cewa shi ma’aiki ne kuma yana da wasu karfin iko masu tarin yawa, wadanda yake bayyanawa a wajen bauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel