San barka: Jaruma Rahama Sadau ta kafa gidauniya don samawa almajirai kayan sanyi

San barka: Jaruma Rahama Sadau ta kafa gidauniya don samawa almajirai kayan sanyi

- Sanyin bana dai yazo da tsanani musamman ga kasashen Afirka ta yamma

- Masana sun gano cewa, ba a taba yin matsanancin sanyi irin na wannan shekarar ba

- Jaruma Rahama Sadau ta kaddamar da gidauniyar tallafi ga almajirai don samar musu da kayan sanyi

A lokacin da jama'ar kasashen Afirka ta yamma musamman Najeriya ke fama da tsananin sanyi, wanda masana suka ce anyi shekaru ba a fuskanci irinsa ba, wasu sanannun mutane a Najeriya sun fara yunkurin tallafawa marasa galihu.

Almajirai ne aka fi mayar da hankali a kai don babu mai basu ko rigar arziki balle kuma rigar sanyi.

Sanyin wannan shekarar ya zo da matukar ba zata saboda sanyin ya shafi wuraren da basu saba fuskantar matsanancin sanyin ba.

Shahararriyar jarumar Kannywood mai yawan jawo cece-kuce, Rahama Sadau ta kaddamar da wani asusu na tara kayan sanyi da za a rabawa almajirai a wasu jihohin Najeriya.

Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na tuwita cewa za a raba kayan sanyin ne a jihohin Kaduna, Katsina, Jos, Bauchi, Kano da sauransu.

KU KARANTA: Tirka-tirka: Matar da ta auri maza hudu ta nemi duka su hada kai domin rainon dan da za ta haifa

"Ba zamu iya tallafawa kowa ba amma kowa daga cikin mu zai iya taimakawa wani," a cewar Rahama.

Ta kara da cewa, "babu wata mafificiyar hanya da za a taimaka wa almajirai fiye da samar musu da kayan da zasu rage musu jin sanyi."

Ta yi kira ga mutane a kan kowa ya hada hannu domin tallafawa almajirai, wadanda tace bai kamata a zuba wa ido ba.

Ba wannan ne karo na farko da taurarin Kannywood suka fara tallafawa marasa galihu ba a cikin jama'a.

Taurari irin su Hadiza Gabon, Mansura Isah, Aisha Tsamiya da sauransu sun kasance suna taimakawa jama'a mabukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng