Tirka-tirka: Matar da ta auri maza hudu ta nemi duka su hada kai domin rainon dan da za ta haifa

Tirka-tirka: Matar da ta auri maza hudu ta nemi duka su hada kai domin rainon dan da za ta haifa

- Hada abokan mu'amala ta aure masu yawa kowa ya sani halin maza ne

- Tory mai shekaru 20 'yar asalin kasar Florida ta kasance masoyiya kuma mai mu'amala da maza hudu

- Suna raba kwanaki a tsakaninsu kuma har ta samu juna biyu wanda suka amince na dukkansu ne

Hada abokan mu'amala a rayuwa dai ana danganta shi ne da maza. Wannan kuwa wata jarumta ce da cikar isa wacce ubangiji ke basu.

A nan kuwa wata mace ce me kamar maza. Ta yi mu'amala tare da maza hudu kuma ta samu juna biyu. Sunyi alkawarin rayuwa tare da kuma tarbiya da kula da dan in an haifa.

Tirka-tirka: Matar da ta auri maza hudu ta nemi duka su hada kai domin rainon dan da za ta haifa
Tirka-tirka: Matar da ta auri maza hudu ta nemi duka su hada kai domin rainon dan da za ta haifa
Asali: Facebook

Tory Ojeda mai shekaru 20 daga Florida ta hadu da saurayinta na farko ne mai suna Marc lokacin da tana makaranta. Ta fara mu'amala da Travis mai shekaru 23 bayan watanni biyu. A watan Yuli na wannan shekarar ne ta fara mu'amala da Ethan mai shekaru 22 sai kuma daga baya Chris mai shekaru 22.

KU KARANTA: Tirkashi: Hankalin mutane ya tashi a kasar China bayan sun wayi gari sun ga rana guda 3 ta fito

Tory ta samu ciki a lokacin da taje hutu tare da Chris. Hakan ne yasa ya zamo uban cikinta amma kuma duk mazan hudu zasu kula da abinda zata haifa.

A halin yanzu Tory na kasancewa da abokan mu'amala daban-daban. Tana rayuwa da dukkansu. Kowa yana da dakinshi amma suna raba kwana da Tory.

Duk da ta ce dan zai tashi yana kallon maza hudu a matsayin mahaifanshi, amma hakan ba karamin jin dadi bane gareta.

Mazan hudu sun bayyana tsananin jin dadinsu saboda sun kusa zama iyaye ga dan masoyiyarsu Tory.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng