Yaki da ta’addanci: Magu ya yi ma barayin dukiyar jama’a sabon albishir a 2020

Yaki da ta’addanci: Magu ya yi ma barayin dukiyar jama’a sabon albishir a 2020

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Malam Ibrahim Magu ya bayyana cewa zasu dauki sabin tsauraran matakai a kan barayin dukiyar jama’a, musamman barayin mai a yankin Neja Delta.

Magu yace idan suka kammala dabbaka sabbin tsauraran matakan nasu, barayin ba zasu sake samun wani katabus na yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa ba, musamman a cikin sabuwar shekarar 2020.

KU KARANTA: Za mu debi sabbin ma’aiakata da suka cancanta a NAFDAC – Shugabar NAFDAC

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Magu ya bayyana haka ne yayin ziyarar daya kai ofishin EFCC dake garin Fatakwal na jahar Ribas, inda ya gargadi ga barayin mai da masu fasa bututun mai da suka daina ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya fitar, Magu yace: “Bari na yi amfani da wannan daman a gargadi barayin mai masu fasa bututun mai da su daina wannan mugun aiki, a shirye mu ke mu yakesu domin kawo karshen yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa.

“Yankin Neja Delta na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa, don haka hukumar EFCC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar an hukunta dukkanin masu satar mai tare da fasa bututun mai.” Inji shi.

Haka zalika Magu ya kai ziyara zuwa rukunin rundunar Sojan kasa na 6 dake garin Fatakwal inda hukumar EFCC ta ajiye motocin da kotu ta kwace daga hannun barayi ta mika ma gwamnati ta hannun hukumar, inda yace suna cigaba da gudanar da tsarin yin gwanjon motocin.

“Duk motocin da aka kwace su na gwamnati ne, muna cigaba da tafiyar da tsarin, muna bin tsari ne wajen yin gwanjon motocin, ba zamu boye komai ba, duk motocin da muka yi gwanjonsu suna nan bamu fitar dasu ba har sai an kammala biyan kudi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel