Zakaran da Allah Ya nufa da cara: An kubutar da yaron kwamishina da yan bindiga suka sace

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: An kubutar da yaron kwamishina da yan bindiga suka sace

Dakarun rundunar Yansandan Najeriya sun ceto wani karamin yaro dan shekara 6, wanda Dan kwamishinan ruwa na jahar Bayelsa ne, Mista Nengi Talbot Tubonah, bayan kwashe makonni uku a hannun yan bindiga.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito makonni uku da suka gabata ne yan bindigan suka kutsa cikin gidan kwamshinan dake unguwar Opolo cikin birnin Yenagoa na jahar Bayelsa, inda suka yi awon gaba da yaron.

KU KARANTA: Za mu debi sabbin ma’aiakata da suka cancanta a NAFDAC – Shugabar NAFDAC

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: An kubutar da yaron kwamishina da yan bindiga suka sace
Yaron da barawon
Asali: Facebook

Rundunar Yansanda na musamman, Operation Puff Adder ce ta gudanar da aikin ceton yaron a cikin yankin Karamar hukumar Ijaw ta kudu, sa’annan Yansanda sun samu nasarar kama jagoran masu garkuwan.

A wani labari kuma, da alama dai har yanzu tsuguni bata kare ba, sakamakon wani rahoto daya tabbatar da wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da sabon farmaki a karamar hukumar Malumfashi ta jahar Katsina.

Miyagun sun kai samamen ne da yammacin Litinin, 6 ga watan Janairu ga wasu al’ummomin karamar hukumar Malumfashi, wanda hakan yasa jama’a da dama tserewa daga muhallansu domin tsira da ransu.

Sai dai a sakamakon harin wani malamin jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, wanda ke koyarwa a cibiyar horas da daliban da suka kammala karatun sakandari kafin su shiga jami’a, SBRS, ya gamu da ajalinsa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta tabbatar.

Amma rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina ta tura jami’an zuwa inda lamarin ya auku domin fuskantar yan bindigan, inda suka dinga musayar wuta a tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel