Anambra: Zan yi wa kowane bangare adalci a fadin Kasar nan – Inji Buhari

Anambra: Zan yi wa kowane bangare adalci a fadin Kasar nan – Inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tabbatar da shirinsa na daukar kowane bangare a kasar nan daya ba tare da nuna banbancin ba.

Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai zama mai adalci ga kowa ba tare da la’akari da wani banbancin akida da ra’ayin siyasa ba.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne wajen kaddamar da wasu ayyuka da aka yi a Garin Umunze domin maganin zaizayewar kasa.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust, gwamnatin tarayya ta yi wannan aiki ne a kan wani titin Kudancin Garin Orumba a Jihar Anambra.

Karamar Ministar muhalli ta Najeriya watau Misis Sharon Okeazor ce ta wakilci shugaban kasar a wajen bude wannan aiki da aka yi a jiharta.

KU KARANTA: Siyasa: Fadar Shugaban kasa ta ja-kunnen Kungiyar CAN

Anambra: Zan yi wa kowane bangare adalci a fadin Kasar nan – Inji Buhari
Shugaban kasa Buhari ya yi alkawarin yi wa kowa adalci
Asali: UGC

“Wannan gwamnatin ta wa ta yi alkawari cewa babu wani yanki na kasar nan da za ayi watsi da shi saboda banbancin shiyya ko kuma siyasa.”

“Na ci burin daukar kowa daya a kasar nan. Kuma zan cigaba da yin gaskiya ga kowane yanki na fadin Najeriya.” Inji Shugaban kasa Buhari.

Ministar a madadin shugaban kasar ta bayyana cewa matsalar zaizayewar kasa ya na cikin manyan kalubalen da Anambra ta ke fuskanta.

Buhari ya ja kunnen mutanen Gari su daina jefar da bola a kan hanya, wanda a cewarsa, ya na cikin abubuwan da ke sa kasar yankin ta cinye.

Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ta bakin Mataimakinsa, ya yabawa kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na kokarin ceto jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel