Trump ya yi amai ya lashe kan barazanar kai hari wuraren tarihi a Iran

Trump ya yi amai ya lashe kan barazanar kai hari wuraren tarihi a Iran

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Talata ya janye barazanar da ya yi na kai hari a wuraren tarihi a Iran idan Iran ta mayarwa Amurka martani saboda kashe daya daga cikin manyan dakarun sojojin ta, Qassem Soleimani kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

Kai hari a wuraren tarihi yana daya daga cikin laifin yaki.

A ranar Asabar ne Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Amurka ta gano wuraren 52 a Iran ciki har da wurare da ke da matukar muhimmanci ga al'addun Iran da za ta kai hari muddin Iran ta kai hari a Amurka ko wuraren da Amurka ke da kayayyakin ta.

Trump ya wallafa sakon na Twitter ne yayin da wutar rikici tsakanin kasashen biyu ke kara ruruwa bayan umurnin kashe kwamandan sojojin tsaro na musamman Qassem Soleimani a Iraq.

A yayin da ya ke magana da 'yan jarida a ofishin shugaban kasa wato Oval Ofis a ranar Talata, Trump ya shaida musu karara cewa zai bi dokokin yaki.

Ya ce: "Toh, idan haka doka ya ce, Ina son inyi biyaya ga doka. Amma ku tuna fa: Suna kashe mutanen mu, suna tarwatsa mutanen mu amma mu dole mu lalaba wuraren tarihinsu. Bani da matsala da hakan. Ba matsala."

Ya kara da cewa: "Idan Iran ta aikata wani abinda bai kamata ta aikata ba, tabbas za su gamu da sakamakon abinda suka aikata ba tare da sasauci ba."

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

A ranar Litinin, sakataren tsaron Amurka, Mark Esper ya nuna cewa sojojin Amurka ba za su sabawa dokokin yaki ba ta hanyar lalata wuraren tarihi Iran.

Da aka tambaye shi ko zai kai hari wuraren al'adu, Esper ya shaidawa manema labarai na gidan gwamnati cewa: "Za mu bi dokokin yaki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel