Sai dana sha kukana na more lokacin da aka biya ni albashina na farko a kasar Saudiyya - Likita dan Najeriya
- Wani likitan Najeriya da ya koma kasar Saudi Arabia ya bayyana yadda ya fashe da kuka bayan da ya karba albashin shi na farko
- Ya ce a Najeriya yana duba marasa lafiya a kalla 100 zuwa 120 a rana amma ana biyanshi N118,000
- Amma albashin shi na farko a kasar waje an bashi $4,500 a watan farko da yayi a kasar Saudi Arabia
Wani likitan Najeriya da ya koma kasar Saudi Arabia ya bayyana yadda ya fashe da kuka bayan da ya karba jimillar albashinshi na watanni hudu Najeriya a kasar dake tsakiyar gabas din.
Bayan barin aikinshi a Najeriya, likitan ya wallafa yadda ya gane tsananin aikin tikin da yayi a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita.
Ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar ta tuwita kuma likitan, ya ce yana karbar N118,000 a matsayin albashinshi na wata daya a Najeriya. Hakazalika, yana duba marasa lafiya daga 100 zuwa 120 a kowacce rana.
Amma kuma bayan 2014 da ya koma kasar Saudi Arabia, an biya shi $4,500 na ganin a kalla marasa lafiya biyar zuwa bakwai a rana.
KU KARANTA: Garin dadi na nesa: Mutum 1 ne kacal ya mutu a birnin Oslo sanadiyyar hadarin mota a shekarar 2019 baki daya
Ga abinda ya wallafa: “A shekarar 2013 a Najeriya, ina aiyuka biyu ne. Safe da dare kuma ina ganin marasa lafiya a kalla 100 zuwa 120 a matsayina na likita. A karshen wata ina karbar N118,000.”
Ya kara da cewa:”Bayan da na gana intabiyu a kasar Saudi Arabia, sai aka tambayeni nawa za a dinga biya. Mamaki kuwa ya kama ni tun daga nan. A karshen wata kuwa sai aka biya ni $4,500. Jimillar albashi na kenan na watanni hudu. Ina duba marasa lafiya biyar zuwa bakwai a rana daya.”
Likitan ya kara da cewa fashewa yayi da kuka yayin da ya samu wannan albashi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng