Garin dadi na nesa: Mutum 1 ne kacal ya mutu a birnin Oslo sanadiyyar hadarin mota a shekarar 2019 baki daya

Garin dadi na nesa: Mutum 1 ne kacal ya mutu a birnin Oslo sanadiyyar hadarin mota a shekarar 2019 baki daya

- Mutum daya kacal ne aka gano ya rasu a hatsarin Oslo na kasar Norway a 2019

- Wannan ne karo na farko da ba a samu mutuwar kananan yara masu kasa da shekaru 16 ba a titunan kasar

- Hadurran sanadin cunkoson ababen hawa kuwa sun fi yawa ne a titunan kasashen Bulgaria da Romania

Mutum daya kacal ne ya mutu sakamakon hatsarin da aka samu daga cunkoson ababen hawa da aka yi a Oslo a 2019, kamar yadda jami’ai suka bayyana. Wannan ne karo na farko da ba a samu mutuwar yara masu kananan shekaru ba a cunkoson ababen hawa na Norway a tsawon shekara.

Amma kuma, mutane masu tarin yawa sun rasa rayukansu a sauran kasashe a wannan shekarar. A shekarar 2018 an samu mutane 108 ne da suka rasa rayukansu amma a 2019 an samu mutane 110.

Wata kafar yada labarai ta cikin gida ta ruwaito cewa, mafi karancin yawan hadurran da aka samu na cikin gida an same su ne 2017, lokacin da mutane uku suka mutu a babban titin Oslo.

Kamar yadda titunan Norway suka nuna, hukumomin sun bayyana cewa a shekaru 50 da suka gabata, yawan mamatan da ake samu a hadurran sun ragu ba kadan ba. Daga mutane 41 a 1975 zuwa daya tak a 2019.

Norway ce ke da mafi karancin mace-mace da ake yi a hadurran cunkoson kan titi a Turai a 2017, an samu mutane 20 da suka rasa ransu a cikin mutane miliyan daya dake kasar.

KU KARANTA: Yadda aka dauki bidiyon wata budurwa tana lalata a bainar jama'a bayan ta sha giya ta bugu

Idan aka danganta, mutane 126 ne suka rasu a kan titunan birnin London a 2019 daga farkon shekara zuwa watan Disamba . An samu karin mutane 22 zuwa shekarar 2018.

Duk da haka kuwa, ana ganin UK a matsayin kasa mafi karancin yuwuwar hadarin ababen hawa a titunanta. Ana samun mace-mace 30 cikin mutane miliyan daya a shekara.

Mafi hatsarin tituna kuwa sune na kasashen Bulgaria da Romania, wadanda ake samun a kalla mace-macen mutane 90 cikin miliyan daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel