Yanzu-yanzu: Sadio Mane ne gwarzon dan kwallon Afrika na shekara (Jerin gwarazan 2019)

Yanzu-yanzu: Sadio Mane ne gwarzon dan kwallon Afrika na shekara (Jerin gwarazan 2019)

Dan wasan kungiyar Liverpool kuma dan kasar Senegal, Sadio Mane, ya zama gwarzon dan kwallon nahiyar Afrika na shekarar 2019 a taron bikin da aka shirya ranar Talata, 7 ga watan Junairu, a kasar Masar.

Dan shekara 27 yayi takara da abokin wasansa a Liverpool, Mohamed Salah da dan kwallon Manchester City, Riyad Mahrez.

Ga jerin gwarazan:

Gwarzon dan kwallon Afrikan shekara

Sadio Mane (Senegal da Liverpool)

Gwarzuwar yar kwallon Afrikan shekara

Asisat Oshoala (Nigeria & Barcelona)

Matashin dan kwallon shekara

Achraf Hakimi (Morocco & Borussia Dortmund)

Kocin Afrikan shekara (Maza)

Djamel Belmadi (Algeria)

Kocin Afrikan shekara (Mata)

Desiree Ellis (South Africa)

Gwarzuwar kasar shekarar 2019

Algeria

Dan kwallon da yaci kwallo mafi kyau a shekara

Riyad Mahrez

Yan kwallo 11 mafi kyau a Afrika

Andrey Onana, Achraf Hakimi, Kalidou Koulibaly, Joel Matip, Serge Aurier, Riyad Mahrez, Idrissa Gueye, Hakim Ziyech, Mohamed Salah, Sadio Mane, Pierre Emerick-Aubameyang

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel