Yadda wani matashi ya kashe kansa saboda faduwa caca

Yadda wani matashi ya kashe kansa saboda faduwa caca

- Wani mutum mai shekaru 27 a duniya mai suna Meshack Keith Bwisa ya bace tun ranar 25 ga watan Disamba

- An gano gawar saurayin a dakinsa bayan da aka gano ya kashe kansa ne saboda cacar da bai yi nasara a kai ba

- Jami'an 'yan sanda sun ga wasiyyarsa bayan da aka balle kofar dakin Bwisa inda gawarsa ke kwance

Wani mutum mai shekaru 27 a duniya mai suna Meshack Keith Bwisa, an gano ya mutu bayan da aka gano ya bace a ranar 25 ga watan Disamba.

An gano cewa mamacin yana aiki ne da hukumar kula da kudin shiga ta kasar Kenya dake Kakamega. An gano gawarsa ne bayan da 'yan uwansa suka je har gidansa saboda sun hada bikin murnar sabuwar shekara a gidan.

An gayyaci jami'an 'yan sanda bayan da aka bige kofar dakin aka balle ta. An ga tokar gawayi a tsakar dakin, lamarin da ke nuna cewa Bwisa ya mutu ne saboda gubar iskar Carbon monoxide.

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Babban jami'in 'yan sandan yankin Kakamega, David Kabena ya bayyana cewa, wanda ya rasun ya bar wasiyyar cewa rashin nasara a cacar da yayi ce ta sa ya kashe kansa.

Ya ce: "Har gawar ta kumbura kuma ta fara rubewa. Akwai yuwuwar cewa Bwisa ya rasu ne a ranar 25 ga watan Disamba, 2019."

"An samu wasiyyar da ya rubuta kuma a ajiye a kan gawarsa. A wasikar, Bwisa ya bayyana bacin ransa na rashin nasarar cacar da ya shiga. Wannan ne kuwa dalilinsa na kashe kansa. Ya kara da shawartar matasa da 'yan uwansu da su guji caca don kuwa tana talauta mutane ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel