Yanzu-yanzu: Boko Haram na kai hari yanzu wurin da Sojojin Chadi suka janye a Borno

Yanzu-yanzu: Boko Haram na kai hari yanzu wurin da Sojojin Chadi suka janye a Borno

Yan ta'addan Boko Haram na kan kai hari garin Munguno, barikin Sakta 3 a jihar Borno. The Cable ta ruwaito.

Sojojin Chadi 1200 da suka bar Najeriya makon nan suke amfani da barikin kafin suka janye daga kasar.

An samu tabbacin harin daga majiyoyin Sojoji akalla biyu cewa ana artabu.

Daya daga cikin majiyar yace: "Yan ta'addan sun dira garin misalin karfe 7 na yamma; sun zo da motocin yaki kuma ana artabu yanzu haka."

Ku saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel