An kashe mutum daya yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Imo
Rahotanni sun kawo cewa an kashe wani matashin mutum mai suna Amajuru Ahamefule a ranar Litinin a karamar hukumar Isu da ke jihar Imo.
An harbi Ahmefule har lahira a lokacin wani rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar.
Kakakin yan sandan jihar Imo, Orlando Ikeokwu wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan wasu shugabannin kananan hukumomi da Gwamna Emeka Ihedioha ya dakatar sun yi ikirarin samun wani hukunci na kotun koli.
Ikeokwu ya kuma bayyana cewa rundunar yan sanda a jihar bata rigada ta samu kowani umurni daga kotu kan lamarin ba.
A cewar shugabannin kananan hukumomin, hukuncin kotu ta basu damar karbar shugabanci daga hannun kwamitin wucin-gadi da Gwamnan ya kafa a dukkanin kananan hukumomin jihar.
Kakakin yan sandan ya kara da cewa matakin karbar shugabanci ta karfin tuwo da shugabannin kananan hukumomin suka yi ya hadu da cikas inda mambobin kwamitin wucin-gadin kuma magoya bayan PDP suka nuna adawa.
KU KARANTA KUMA: Abun al’ajabi: Wani katoton karfe ya rufto daga sararin samaniya a Nijar
Hakan ya yi sanadiyar barkewar rikici sannan ana ta harbi ba kakkautawa a sama.
Mutane da dama sun jikkata sannan aka harbe Ahemefule har lahira cikin hakan.
Mista Ikeokwu ya kara da cewa tuni kwamishinan yan sandan jihar Imo ya shiga lamarin sannan an kaddamar da bincike a kai.
Ya shawarci bangarorin da su ajiye takobinsu sannan su bi doka da oda domin guje na ci gaban karya doka a jihar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng