Buhari yana ganawa da shugaban INEC a Villa

Buhari yana ganawa da shugaban INEC a Villa

- Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata 7 ga watan Janairu ya gana da shugaban INEC da Sufeta Janar na 'Yan sandan Najeriya

- A jawabin da ya yi yayin ganarwarsu, Shugaba Buhari ya shaidawa shugaban INEC ya tabbatar ya yi aikinsa bisa doka ba tare da tsoro ko son kai ba yayin zabe

- Da ya ke magana da shugaban 'yan sanda, Shugaba Buhari ya ce yana son 'yan sanda su samar da tsaro yayin zabe ba tare da nuna son kai ba

Shugaba Muhammadu Buhari a halin yanzu yana ganawa da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da tawagarsa a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya a Abuja.

A halin yanzu dai ba san dalilin ganawar ta su ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai a sakonsa na sabuwar shekara, Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa na taimakawa da karfafa dokokin zabe a Najeriya da kasashen Afirka ta Yamma da za su gudanar da zabukansu a wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Da ya ke magana da shugaban 'yan sanda, Shugaba Buhari ya ce yana son 'yan sanda su samar da tsaro yayin zabe ba tare da nuna son kai ba

Ya ce: "Duk wanda za ku sanar a matsayin wadanda suka yi nasara su kasance wadanda mutane suka zabe ne.

"Demokradiyya harka ce ta bawa mutane ikon zaban wanda suke so saboda haka dole a bawa mutane abinda suka zaba. Ka zage damtse, babu batun dabarbaru ko makirci."

Ya ce niyyarsa shine ya bawa 'yan Najeriya hukumar zabe da ke da inganci kamar yadda ake samu a sauran kasashen duniya kuma ya umurci shugaban hukumar zaben ya kasance mai biyaya ga dokokin zaben da adalci.

Da ya ke magana da shugaban 'yan sandan, ya ce abinda ya ke so shine samar da tsaro ba tare da bangaranci ko son kai ba.

Ya ce: "Ya zama dole a gudanar da zaben mu cikin zaman lafiya da lumana. Dole a gudanar da zaben cikin adalci ba tare da magudi ba ko razana mutane. Aikin 'yan sanda ne su tabbatar da hakan kuma abinda na ke tsamanin samu kenan daga yanzu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel