Jami'an tsaro a filin jirgin sama a Kano sun tsare motar kwamanda bayan sun zane 'yan Hisbah

Jami'an tsaro a filin jirgin sama a Kano sun tsare motar kwamanda bayan sun zane 'yan Hisbah

A ranar Litinin ne jami'an tsaro a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano dake birnin Kano suka tsare motar babban kwamandan rundunar Hisbah, Mohammad Ibn-Sina, bayan sun zane wasu dakarun Hisbah biyu.

Lamarin ya faru ne sakamakon dugunzuma jami'an tsaro mallakar hukumar kula da filayen jirgn sama na kasa (FAAN) da wasu hadiman Ib-Sina suka yi yayin da suka je filin jirgin saman domin dauko shi.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron filin jirgin sun yi wa dakarun Hibah biyu taron dangi tare da kulle su bayan sun zane su yayin da suke cikin kakinsu na 'yan Hisbah.

Sabani ya shiga tsakanin jami'an tsaro na FAAN da na Hisbah ne a kan wurin ajiye motar Ibn-Sina a filim jirgin saman..

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa rai ya baci ne sakamakon kin biyayyar da hadiman Ibn-Sina suka yi yayin da jami'an FAAN suka umarcesu da su ajiye motar shugaban nasu a wurin ajiye motoci na kudi, amma suka ki.

Jami'an tsaro a filin jirgin sama a Kano sun kwace motar kwamanda bayan sun zane 'yan Hisbah
'Yan Hisbah
Asali: Facebook

Tirjewar jami'an Hisbah ta jawo cacar baki mai zafi a tsakaninsu da jami'an FAAN' lamarin da ya kai har an bawa hammata iska, a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Mutane 8 masu karfin iko a gwamnatin Buhari

Dakarun Hisbah sun isa filin jirgin saman ne domin dauko shugabansu wanda jirginsa zai sauka da misalin karfe 2:00 na rana.

Sai dai, kokarin manema labarai na jin ta bakin mahukuntan filin jirgin sama ya ci tura, kasancewar sun ki yin magana da wakilan jaridu.

Lawan Ibrahim, kakakin rundunar Hisbah, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da daukan alkawarin bayar da cikakken bayani a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel