Tirkashi: Kamfani na tilasta ma'aikatansa na cin kifi mai rai da kuma shan jinin kaji

Tirkashi: Kamfani na tilasta ma'aikatansa na cin kifi mai rai da kuma shan jinin kaji

- Wani kamfanin siye da siyarwar kayan ginin gidaje a kasar China ya tilasta ma’aikatan shi da cin kifi mai rai da kuma shan jinin kaji

- Kamar yadda manajan kamfanin ya bayyana, hakan ya kasance ladabtarwa ne ga ma’aikatan don kuwa sun kasa cimma burin kamfanin na watanni hudu

- Wata tsangayar ‘yan kwadago dake kasar ta ce tabbas za a binciki kamfanin kuma matukar aka kama su da wannan laifin za a hukunta su

Wani kamfanin siye da siyarwa dake Guizhou a kasar China ya ladabtar da ma’aikatansa ta hanyar tilasta musu cin kifi mai rai da shan jinin kaji saboda rashin cika sharuddan aiki da suka yi.

Rahoton ya bayyana cewa, wannan mummunar ladabtarwa da aka yi wa ma’aikatan shagon siyar da kayan ginin ta janyo muhawara a shafukan intanet lokacin da aka wallafa bidiyon.

Bidiyon ya nuna yadda wani ma’aikaci yake ciro kifi mai rai yana mika wa ma’aikatan tare da umartarsu da su ci da ranshi. Sannan bidiyon ya nuna wadansu kuma suna shan jini wanda aka kyautata zaton jinin kaji ne.

A cikin rahoton, an bayyana kakakin kamfanin na cewa, ma’aikatan ne suka sa kansu a aikin ba tare da wani ya tilasta su ba.

KU KARANTA: Garin dadi na nesa: Gwamnatin kasar Finland za ta kawo tsarin aikin kwana 4 a mako, sannan aikin awa 6 a kowacce rana

Wani wakilin kamfanin da ake siyar da kayan ginin ya ce wannan ladabtarwa ta rutsa da ma’aikatan kamfanin 20 ne wadanda suka gaza sayar da hajar kamfanin a rubu’in shekara. Sannan su ma’aikatan ne suka kirkiri wannan hanyar ladabtarwa ta hanyar cin kifi mai rai da shan jinin kaji. Sun ce hakan zai kara musu kaimi wajen zage damtse don cika burin kamfanin nan gaba.

Bayan wallafa rahoton a bidiyo, wata tsangayar ‘yan kwadago ta bayyana wa manema labarai cewa, ta fara binciken yadda abin ya faru. Idan aka samu kamfanin ko manajan da bada umarnin ga ma’aikatan, toh tabbas za a hukunta shi yadda ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel