'Yan bindiga sun kashe sojoji 4 tare da sace Turawa fatake 3

'Yan bindiga sun kashe sojoji 4 tare da sace Turawa fatake 3

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton cewa tsagerun yankin Neja-Delta ne sun kashe sojojin ruwa hudu tare davsace wasu bakin Turawa fatake dake aikin yasar kogi a karamar hukumar Ekeremor, jihar Bayelsa.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin fataken bakin hauren da 'yan bindigar suka sace akwai biyu 'yan kasar Rasha da guda daya dan kasar Indiya.

Daily Trust ta rawaio cewa majiyarta ta sanar da ita cewa lamarin ya ne a yankin garin Agge dake karkashin jihar Delta, kuma sojojin da aka kashe ma sun fito ne daga bataliyar NNS a jihar Delta.

Wata majiya daga cikin mazauna yankin da abin ya faru, wacce ta nemi a boye sunanta, ta sanar da Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma'a, tare da bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe sojojin hudu bayan musayar wuta na tsawon sa'o'i.

'Yan bindiga sun kashe sojoji 4 tare da sace Turawa fatake 3
Sojojin ruwa
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa daya daga cikin 'yan bindgar ya rasa ransa yayin musayar wuta da sojojin.

DUBA WANNAN: Soja ya kashe mutane biyu da sharbebiyar wuka, ya raunata wasu da yawa a cikin barikin sojoji

Mazauna yankin sun shiga cikin zulumi da zaman dar-dar bayan samun labarin cewa dakarun soji na shirin kai hari yankin domin ganin sun kama 'yan bindigar da suka kashe abokan aikinsu, kuma suka sace bakin hauren fataken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel