Ita Enang: ‘Yan Najeriya da-dama sun samu aikin yi a sakamakon rufe iyakoki”

Ita Enang: ‘Yan Najeriya da-dama sun samu aikin yi a sakamakon rufe iyakoki”

Fadar shugaban kasar Najeriya, ta fito ta yi magana game da rufe iyakokin kasa da aka yi tun watannin baya saboda wasu dalilai.

A cewar fadar shugaban Najeriyar, da yawan mutane sun samu sana’a a sakamakon garkame duk wasu iyakokin Najeriya na kan kasa.

Sanata Ita Enang ya bayyana cewa mutane birjik wanda a baya ba su da aikin yi, sun rungumi harkar noma a wannan gwamnatin.

A cewar Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin Neja-Delta, mutane sun shiga noman shinkafa, rogo da gero da sauransu.

Ita Enang ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke amsa tambayar da ‘Yan jarida su ka yi masa game da rufe iyakokin da aka yi.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta yi alkawarin ceto mutane daga talauci a 2020

Ita Enang: ‘Yan Najeriya da-dama sun samu aikin yi a sakamakon rufe iyakoki”
Ita Enang ya ce kulle iyaka da aka yi alheri ga 'Yan Najeriys
Asali: Twitter

Enang ya lissafowa ‘Yan jarida irin amfanin da musamman Matasa su ka gani bayan gwamnatin Najeriya rufe duk wasu iyakokin ta na kasa.

Bayan babbako da aikin noma, Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa wannan mataki ya sa kudin shigar da Najeriya ta ke samu ya karu.

Sanata Enang ya yi kira ga gwamnonin Kudu maso Gabashin kasar su mara baya ga matakin nan da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka.

Tsohon Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar majalisa ya ce Buhari ya cancanci yabo na kawo zaman lafiya da kuma samar da abinci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel