Ragas: Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’addan Boko Haram 6, an kashe musu 4

Ragas: Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’addan Boko Haram 6, an kashe musu 4

Dakarun runduna ta 29 ta rundunar sojan kasa ta Najeriya ta hallaka mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram guda shida a wani arangama da suka kwasa da juna a kauyen Jakana na karamar hukumar Konduga na jahar Borno.

Jaridar The Cables ta ruwaito Sojoji da Boko Haram sun yi wannan arangama ne a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu inda aka kusan yin ragas, sakamakon Sojoji sun kashe yan ta’adda shida, Boko Haram kuma ta kashe Sojoji 4.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bude wuta a Malumfashi, sun bindige Malamin SBRS har lahira

Wata majiya ta bayyana yan Boko Haram sun fara rufe manyan hanyoyin garin, daga nan suka nufi sansanin Sojoji inda suka yi fito na fito da Sojoji. Shi ma wani direban motar haya, Bukar Mala ya bayyana cewa da kyar ya sha bayan wani dan ta’adda ya nemi ya harbi tayar motarsa.

Direba Mala ya tabbatar ma majiyar Legit.ng da cewa tun a ranar asabar aka fara dauki da ba dadi tsakanin yan ta’addan Boko Haram da dakarun Sojojin Najeriya har zuwa tsakar daren Litinin.

Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar, mai kula da sashin labarun rundunar Soja Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ya bayyana cewa: “A ranar 4 ga watan Janairu wasu yan ta’adda sun yi kokarin afka ma sansanin Sojoji dake Jakana, amma Sojoji sun samu galaba a kansu.

“Yan ta’addan sun kai harin ne cikin motocin masu dauke da bindigu guda 6, da wasu kuma a kasa, amma Sojojinmu sun nuna jarumta wajen fin karfin yan ta’addan tare da tarwatsasu, inda suka kashe guda 6, sa’annan suka kama makamai.

“Amma akwai Soja guda daya rigamu gidan gaskiya, da wasu guda biyu da suka samu rauni. Tuni an garzaya da wadanda suka jikkatan zuwa asibiti inda suke samun kulawa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel