Buhari ba zai zakulo Magajinsa da hannunsa ba – Inji Fadar Shugaban kasa

Buhari ba zai zakulo Magajinsa da hannunsa ba – Inji Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari, ba zai zakulo wanda zai gaje kujerarsa a zaben shekarar 2023 ba.

Shugaban kasar ya maida martani ga kiran da Fasto Tunde Bakare ya yi a makon jiya na cewa Buhari ya fito da Magajinsa da kansa.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakinsa, Mista Femi Adesina a Ranar Litinin.

Da ya ke jawabi a shirin siyasar Politics Today da ake yi a gidan talabijin na Channels TV, Hadimin, ya ce zabe zai yi aiki a 2023.

Adesina ya ce: “Zuwa Mayun 2023, da yardar Ubangiji, ya kammala wa’adinsa biyu a matsayin shugaban kasa, ba zai sake takara ba.”

KU KARANTA: 2023: Watakila DSS ta binciki wasu ‘Yan riga-Malam-masallaci a PDP

Buhari ba zai zakulo Magajinsa da hannunsa ba – Inji Fadar Shugaban kasa
Buhari ya fadawa Bakare ba zai fito da Magajinsa da kan sa ba
Asali: Twitter

“Zai bar mulki, ya san wannan a ransa. Bakare ya ce ya kamata (Buhari) ya damu da ganin wanda zai gaje shi, eh wannan haka ne.”

“Amma ba zai murde zaben domin ya zabi wanda zai hau kujerar ba. Ba zai dauko wanda zai zama shugaban kasa da hannunsa ba.”

Mun san sa, ba haka ya ke ba. Zai damu da ganin wanda zai zama shugaba? Eh. Zai tabbatar da ganin an yi zaben gaskiya da adalci.”

Femi Adesina ya tabbatar cewa babu wanda zai yi amfani da kudi wajen samun mulki, sannan kuma za a sa hannu a sabuwar dokar zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng