Zabuka, shirin 2023, karin haraji da sauran abubuwan da za a gani a 2020
Jaridar nan ta Daily Trust ta tattaro jerin duk wasu manyan batutuwa da za ci karo da su a wannan sabuwar shekarar. Legit.ng Hausa ta tsakuro wasu daga ciki, ta kawo maku.
1. Zaben Edo da Ondo
A bana za ayi zabubbukan gwamnoni a Jihohin Edo da Ondo. A duka jihohin APC na ke mulki, amma ana tunanin za a yi gumurzu wajen samun tikitin jam’iyyar kafin a kara a waje.
2. Atiku da Tinubu
A cikin wannan shekara da aka shiga ne Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Tinubu za su dage wajen wanke allonsu a PDP da APC. Ana ganin cewa ‘Yan siyasar su na harin zaben 2023.
3. Sauya-sheka
Yayin da ake dumfarar 2023, za a rika jin labarin cewa ‘yan siyasa sun canza jam’iyya. Wasu za su bar PDP da APC ko kuma a kafa wata sabuwar jam’iyyar ko kuma a farfado da irinsu PRP.
4. Zaben Amurka
A wannan shekara ne Donald Trump zai nemi zarcewa a kan mulkin kasar Amurka. Yanzu haka dai akwai yunkurin da ake yi a Majalisar Tarayya na sauke shi daga kan karagar mulki baki daya.
5. Shari’ar Dasuki da Sowore
Bayan gwamnati ta ga dama ta fito da Sambo Dasuki da Yele Sowore, za a cigaba da shari’a da su a kotu. Akwai kuma manyan shari’ar da ake yi da irin su Ibrahim Zakzaky da sauransu.
6. Kannywood
2020 babbar shekara a wajen ‘Yan wasan Kannywood da sauran Mawakan Najeriya bayan ficen da Burna Boy ya yi. A bana ne za a fito da sabon fim din da Nafisa Abdullahi ta bada umarni.
7. Kashe-kashe
Rikicin Makiya da Manoma da satar mutane ana garkuwa da su har sai an biya fansa, bai kare ba. Amma ana sa ran cewa an kusa ganin karshen rikicin Makiyayan da aka yi ta fama da shi.
KU KARANTA:
8. Boko Haram
Wani rikicin da ba a gama fama da shi ba a 2019 shi ne na Boko Haram. A shekarar nan da ake ciki ne Sojojin Najeriya za su janye Dakarunsu daga yankin da aka yi galaba a kan ‘yan ta’adda.
9. Karin haraji
A 2020, harajin da ‘Yan Najeriya su ke biya zai karu a sakamakon karin harajin kayan masarufi na VAT da aka yi. Akwai kuma batun karin kudin wuta. Amma an yi karin albashi a fadin kasar.
10. Bashi
Tulin bashin da ke kan Najeriya zai cigaba da yin gaba musamman idan majalisa ta ba shugaban kasa damar aro wasu kudi. Akwai kuma makukun kudi da ake batarwa kan tallafin fetur.
11. Shekaru 50 da yakin Biyafara
A Watan Junairun nan za a cika shekaru 50 daidai da aka tsagaita wutan yakin basasa na Biyafara.
12. Noma
Har ila yau a cikin wannan shekara ne Najeriya ta ke sa ran ganin nasarar Manoma musamman wajen harkar shinkafa da noman auduga a sakamakon matakin da aka dauka na rufe iyakoki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng