Aisha Buhari ta taya Amina Mohammed murnar kyautar da aka ba ta a Duniya

Aisha Buhari ta taya Amina Mohammed murnar kyautar da aka ba ta a Duniya

Kwanakin baya ne aka ba Amina J, Mohammed kyauta a matsayin shugabar Duniya a wani gagarumin biki da aka yi a Landan na kasar Birtaniya.

Uwargidar Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta yi magana game da wannan daukaka da ‘Yar kasarta ta samu daga hannun kungiyar ta Duniya.

Aisha Buhari ta taya Amina Mohammed murnar wannan karin girma, ta ce Duniya ta yabawa irin kokarin da wannan ‘Yar Najeriya ta ke yi wa marasa kafi.

Buhari ta ce: “Ina so in mika sakon farin ciki nag a Misis Amina J. Mohammed, mataimakin sakatariyar majalisar dinkin Duniya, yayin da ta samu kyautar…

…Shugannin Duniya a wajen bikin kyautar da Global Citizen ta shirya a Birnin Ladan da ke kasar Birtaniya.” Inji Mai dakin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Mutum 8 da ke da iko a Gwamnatin Shugaba Buhari

Aisha Buhari ta taya Amina Mohammed murnar kyautar da aka ba ta a Duniya
Amina Mohammed ta lashe kyautar shugabannin Duniya
Asali: Depositphotos

“Misis Mohammed ta cika misalin Mutumiyar Najeriya, kuma an yaba da irin jajircewarta wajen kawo cigaba ga mata da kananan yara da marasa galihu.”

“Yayin da na ke taya ta murna, ina kira gareta da ta dage a wajen harkar kare mata da yara daga duk wata hanyar keta masu alfarma da ci masu zarafi.”

Buhari ta aika wannan sako ne a shafinta na dandalin Tuwita a Ranar Lahadi, 5 ga Watan Junairu, 2019, da rana. Jama’a da dama sun maimaita sakon.

Amina Mohammed ta rike Ministar muhalli a Najeriya a farkon wa’adin shugaba Buhari kafin ta samu kujerar mataimakiyar Sakatariya a majalisar UN.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel