Buhari ya canzawa Gidan Soji zani – PDP ta ce an kashe mutane a Jihohi 13

Buhari ya canzawa Gidan Soji zani – PDP ta ce an kashe mutane a Jihohi 13

Babbar Jam’iyyar hamayyar Najeriya, PDP, ta na so shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen kashe-kashen da ake fama da shi.

Jam’iyyar adawar ta na so a canza Hafsun Sojojin Najeriyar ne domin ganin bayan wannan matsalar rashin tsaro da ya ki ci, ya ki cinyewa.

PDP ta ce ba za ta cigaba da zura idanu kawai ba yayin da aka maida Najeriya matattarar jana’iza, sannan mutane na zama cikin tsoron mutuwa ba.

Babban Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, shi ne ya yi wannan jawabi bayan mummunan harin da aka kai a jihar Kogi.

Mista Kola Ologbondiyan a madadin PDP, ya bukaci shugaban Najeriyar ya kawo sababbin jinin da za su ja ragamar Rundunonin jami’an tsaron kasar.

KU KARANTA: Sojoji sun samu wata nasara a kan ‘Yan ta’addan Boko Haram

Buhari ya canzawa Gidan Soji zani – PDP ta ce an kashe mutane a Jihohi 13
PDP ta ce APC ta gaza takaita kashe mutane da ake yi
Asali: Facebook

“PDP ta daura laifin wannan kashe-kashe da tashin hankali a Najeriya ne a kan sakacin tsaro na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

PDP ta kara da: “Game da kuma gazawar gwamnatin Buhari wajen bankado masu kashe Bayin Allah da tada zaune tsaye domin a hukunta su.”

“Jam’iyyurmu za ta iya tuna cewa babu matakin da aka dauka domin hukunta wadanda su ka kashe mutane a Benuwai, Kaduna, Katsina, Bauchi.

PDP ta cigaba da jero jihohin da rikici ya auku a karkashin mulkin APC da: “…Taraba, Yobe, Zamfara, Kano, Neja, Ribas, Ebonyi, Abia sai kuma Kogi.”

Ologbondiyan ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin APC ta maida sha’anin mulki ya zama iyaka fitar da sakonnin ta’aziyya ga wadanda aka kashe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel