Dakaru sun kashe Mayaka, sun ceto mutum 460 daga Boko Haram

Dakaru sun kashe Mayaka, sun ceto mutum 460 daga Boko Haram

Dakarun Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 461 a hannun ‘Yan ta’ddan Boko Haram, bayan sun hallaka wasu Sojojin Mayakan.

Gidan Talabijin na Channels TV ne ya kawo wannan rahoto a Ranar Lahadi, 5 ga Watan Junairu, 2020. Wannan ya faru ne a Arewa maso Gabas.

Sojojin kasar sun yi nasarar kashe ‘Yan ta’addan a hari da binciken da su ka kai a Jakana da Mainok da ke hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Kanal Aminu Iliyasu a wani jawabi da ya fitar, ya bayyana cewa sun kubutar da Maza 100, da ‘Yan mata 154 da kuma wasu kananan yara har 207.

Bayan wadannan dinbin mutane da aka ceto daga ‘Yan ta’adda, Sojojin sun kuma kubuto da wasu kananan yara hudu da ke tsare a hannunsu.

KU KARANTA: Shugaban Amurka Trump ya na yi wa Iran barazanar kai hari

Rundunar sojojin kasar sun samu wannan gagarumar nasara ne yayin da su ka tsare yankin, su ka kai samame domin bankado ‘Yan ta’addan.

Kanal Iliyasu, wanda shi ne shugaban jami’an da ke hulda da Manema labarai a gidan Soja, ya fitar da wannan dogon jawabi a yau Lahadi.

Sojojin Bataliya ta 29 sun bankado ‘Yan ta’addan ne a Ranar Asabar bayan wata arangama har kuma su ka hallaka Mayakan Boko Haram 10.

Dakarun Bataliya na 2, 5, 29 da Sojojin Bataliya ta 159 da ke tsare da titin Damasak zuwa Kareto a karamar hukumar Mobbar sun taka rawar gani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel