Gwamnatin Tarayya ta karbe aikin hanyar Itobe-Ajaokuta-Okene

Gwamnatin Tarayya ta karbe aikin hanyar Itobe-Ajaokuta-Okene

Mun samu labari cewa Gwamnatin tarayya ta karbe kwangilar titin Ajaokuta zuwa Itobe zuwa Garin Okene da ke jihar Kogi.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta karbe wannan aiki da ta bada ne a sakamakon wata matsala da aka samu wajen aikin.

Wani babban jami’in gwamnatin tarayya da ke lura da aikace-aikace, Injiniya Kajogbola Olatunde, ya bada wannan sanarwa a jiya.

Kajogbola Olatunde ya sanar da ‘Yan jarida cewa an dauki wannan mataki ne saboda wasa da aikin da ‘Yan kwangila su ka yi.

Gadar da ta hada Ajaokuta da Garin Itobe ta karye a sakamakon matsalar da aka samu wajen ginin wannan hanya da ake yi.

KU KARANTA: NIMET ta tsinkayo sanyin da za ayi a Arewacin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta karbe aikin hanyar Itobe-Ajaokuta-Okene
Wasa da aiki ya sa Gwamnati ta kashe kwangilar Itobe - Okene
Asali: Facebook

Injiniya Olatunde ya shaidawa Manema labarai cewa kamfanin Scoa da aka ba wannan aiki ba su yi duk abin da ya kamata ba.

A cewar jami’in, za a dauke kwangilar a ba kamfanin da zai yi aikin da gaske saboda kukan da matafiya su ke ta yi da titin.

Olatunde ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya sam ba ta ji dadin irin tafiyar hawainiyar da aka yi wajen yin kwangilar ba.

Ya kuma kara da cewa ‘Dan kwangilar bai nuna cewa zai iya yin wannan babban aiki ba duk da irin tanadin da aka yi masa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel