Sojoji, ‘Yan Sanda, NSCDC ba za su yi aiki da sababbin Dakarun Amotekun ba

Sojoji, ‘Yan Sanda, NSCDC ba za su yi aiki da sababbin Dakarun Amotekun ba

Mun fara samun kishin-kishin cewa Jami’an tsaron Najeriya sun nuna rashin jituwarsu na aiki da Dakarun Amotekun da wasu gwamnonin kasar su ka kafa.

‘Yan Sanda da Rundunar Sojoji da kuma Ma’aikatan NSCDC duk ba za su yi aiki tare da Sojojin kungiyar OPC, da 'Yan kato-da-gora a tafiyar Amotekun ba.

Rundunar tsaron ba su da niyyar aiki da ‘Yan banga da Dakarun sa-kai da Sojojin Agbekoyas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, wajen samar da tsaro.

An shirya cewa Dakarun Amotekun za su fara aiki ne a Ranar 9 ga Watan Junairu domin kawo karshen matsalar tsaro, amma da alamun an samu matsala.

Gwamnonin Yarbawa sun so a kaddamar da shirin ne a Ranar Alhamis mai zuwa, amma wani na-kusa da gwamnan Osun ya ce jami’an tsaro sun janye jikinsu.

KU KARANTA: An sa ranar da Dakarun Amotekun za su soma aiki a Jihohin Yarbawa

Sojoji, ‘Yan Sanda, NSCDC ba za su yi aiki da sababbin Dakarun Amotekun ba
Sabanin Gwamnoni da Jami’an tsaro ya jawo matsala wajen soma aikin sintiri
Asali: UGC

Wani wanda ya ke tare da gwamna Gboyega Oyetola ya shaidawa ‘Yan jarida a boye cewa Jami’an tsaro sun ce wadannan Dakaru da aka kafa ba su san aiki ba.

Jami’an Soji da ‘Yan Sanda su na da ra’ayin cewa ‘Yan Amotekun ba su samu kwarewar da ta dace wajen yin aikin tsaro ba, don haka su ba sa’o’in juna ba ne.

Wani jami’in ‘Yan Sanda a jihar Ogun ya bayyana cewa ba su gamsu da batun fita sintari da mutanen Garin Yarbawan a matsayin Takwara wurin aiki ba.

Sai dai Jihohin Kudu maso Yammacin kasar sun bayyana cewa Dakarun na Amotekun za su rika bibiyar masu laifi ne, sannan su kawo su gaban jami’an tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel